Rikicin addini ya barke a jihar Taraba

Taswirar Najeriya
Image caption Najeriya ta dade tana fama da rikicin addini da na kabilanci

Rikicin addini ya barke a garin Wukari dake jihar Taraba a Arewa maso gabashin Najeriya inda aka wayi gari da harbe harben bindiga da kona dukiyoyi.

Rahotanni daga garin na Wukari sun ce an yi ta kone kone tsawon sa'o'i kafin al'amura suka lafa.

Ko da yake ya zuwa wannan lokaci babu cikakkun alkaluma na hukuma dangane da wadanda suka rasa rayukan su, amma wadanda suka shaida al'amarin sun ce akwai da dama da aka jikkata.

Shi dai wannan rikici ya samo asali ne daga wani masallaci da aka wayi gari a daren jiya aka rusa a harabar ofishin 'yan sanda na yanki dake Wukarin, masallacin da ba'a idda ginawa ba.

Tun kwanaki da suka wuce ne gardama game da dacewa ko rashin haka ta jima da kaurewa musamman tsakanin rukunonin wasu matasan gari, alamrin da daga bisani ya kai ga rusa shi da misalin karfe biyun dare.

Musayar zafafan kalamai da tada jijiyoyin wuya ne suka kai ga rigimar ta yau.

AbdurRazak Yusuf, matashi ne dake zaune a unguwar Mamara a garin na Wukari, ya kuma shaidawa Editan BBC na Abuja Ahmed Idris cewa:

Naga an yi kone kone, jama'a suna gudu kowa na neman yadda zai fake, kuma babu alamun jami'an tsaro.

Ya kara da cewa akwai shaguna da aka kona, sannan kuma har da almajirai.

To amma kwamishinan yan sandan jihar taraba Aliyu Musa yace tun misalin karfe biyun dare suka sami labarin rushe masallacin, to amma yayin da magabata ke taro domin dakile rikicin da ka iya biyo baya ne wani gungun matasa suka kama zanga zangar nuna rashin amincewa da aukuwar lamarin abin da ya kai ga rincabewar al'amura.

A baya garin na Wukari yayi fama da rikicin kabilanci da ya haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.