Shugaban Hukumar FAO na ziyara a Nijeriya

Babban Direktan Hukumar FAO, Jacques Diouf
Image caption Ziyarar Mr Diouf a Najeriya ta zo ne yayin da wasu jihohin kasar ke fama da karancin abinci.

Babban Direktan hukumar samar da abinci da kuma ayyukan gona ta majalisar dinkin duniya, FAO, ya ce suna bukatar dala biliyan ashirin da biyu, nan da shekaru uku masu zuwa, domin magance matsalar karancin abinci a duniya.

Mista Jacques Diouf ya bayyana hakan ne a lokacin ziyarar da ya kai Abuja, babban birnin Tarayyar Nijeriya.

Ya kuma kara da cewa, ya kamata kasashen Afirka su maida niyya wajen shawo kan matsalar karancin abinci, sannan su kara yawan kudaden da suke warewa domin ayyukan noma.

Ziyarar babban Darektan na hukumar FAO a Najeriyar, ta zo yayin da ake hasashen samun fari a kasar, a wannan shekara.