Bukukuwan tinawa da juyin juya halin Faransa

Jami'an tsaron Faransa kan dawaki suna fareti
Image caption Shugabannin kasashen Afirka goma sha biyu ne ke halartar bikin Bastille na bana.

A karon farko, rukunonin soja daga wasu kasashe goma sha ukku na Afirka, wadanda Faransa ta yiwa mulkin mallaka, suna halartar bikin shekara-shekara a birnin Paris, na tunawa da juyin juya halin ranar Bastille.

A ranar sha hudu ga watan Yulin shekara ta 1789 ne, talakawan Faransa suka afkawa gidan kurkukun Bastille, inda sarakunan kasar na lokacin, ke kulle masu adawa da su.

Wannan shine somin tabin juyin-juya hali a Faransar, inda daga bisani aka kawar da mulkin mulukiyya.

Shugabannin kasashen Afirka goma sha biyu ne ke halartar bikin Bastille na bana, cikinsu har da shugaban mulkin sojan Niger, Janar Salou Jibo.

Shugaba Laurent Gbagbo na Cote d'Ivoire bai karbi goron gayyatar ba, yayin da shi kuma shugaban Madagascar, Andry Rajoelina, ba a gayyace shi ba.