Isra'ila ta hana kai kayan agaji zuwa Gaza

Jirgin ruwa dauke da kayan agaji
Image caption Jirgin ruwa dauke da kayan agaji

Isra'ila ta hana kokarin baya bayan nan da masu fafutuka suka yi na kai wani jirgin ruwa shake da kayan agaji zuwa Gaza.

A halin yanzu jirgin ruwan ya doshi kudu zuwa kasar Masar, inda zai shiga tashar jiragen ruwa ta El Arish.

Wani dan jaridar dake cikin jirgin ya ce jiragen sojin ruwan Isra'ila sun hana jirgin da suke ciki karkatawa zuwa Gaza.

Kungiyar Libyar da ta dauki hayar jirgin ruwan ta ce tana son kai wa Gaza, to amma ba za su so tayar da fitina ba.

Makwanni 6 da suka wuce ne dakarun Isra'ila su ka kwace wani ayarin jiragen ruwan dake dauke da kayan agaji zuwa Gaza.

An kashe 'yan Turkiya 9 dake cikin daya daga cikin jiragen ruwan.