A Nigeria ana ci gaba da neman 'yan jaridar da aka yi garkuwa da su

'Yan sandan Nigeria
Image caption 'Yan sandan Nigeria

A Najeriya, ana ci gaba da zaman jiran tsammani dangane da batun lalubo 'yan jaridan kasar da aka sace tun ranar Lahadin da ta gabata.

Rundunar 'yan sandan Nigeria ta ce tana ta yin iya bakin kokarinta game da haka, har ma ta dauko hayar wasu Turawa da na'urori na musamman, domin gano wajen da ake tsare da mutanen da aka sace.

Da ma kuma tun a shekaran jiya ne sufeto janar na 'yan sandan Najeriyar, Mr Ogbonna Onovo, ya tare a jihar Abiya, domin tinkarar lamarin.

A yanzu haka rundunar 'yan sanda ta Nigeriar na cewa suna tsammanin ana tsare da 'yan jaridar ne a wani wuri da ke tsakanin jihohin Abia da Akwa Ibom.

An dai sace 'yan jaridar guda hudu ne da kuma direbansu ranar lahadin da ta gabata, akan hanyarsu ta komawa wuraren aikinsu bayan da suka halarci wani taro na kungiyar 'yan jaridu ta kasa.

Mutanen da suke garkuwa da su sun nemi a basu Naira miliyan 250 gabanin su sako su.