Baraka ta kunno kai akan matsayin kamfanin NNPC

Shugaban Nigeria
Image caption Dr Goodluck Ebele Jonathan

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu an samu baraka a tsakanin wasu mahukunta a kasar, game da takamammen halin da babban kamfanin mai na kasar, wato NNPC, ke ciki.

Wasu manya manyan ministoci biyu a kasar sun musanta ikrarin da minista a ma'aikatar kudi Mr Remi Babalola ya yi cewar, kamfanin ya tsiyace saboda bashin da yayi masa kanta.

Ministan kudi na Nigeria, Mr Segun Aganga, da kuma ministar yada labarai ta kasar, Farfesa Dora Akunyili, sun ce maganar ba haka ta ke ba, domin kuwa babban kamfanin Mai na kasar bai tsiyace ba.

Masana tattalin arziki a Nigeriar na cewa kalamai irin wadannan masu cin karo da juna da mahukuntan ke yi, na iya janyo cikas ga tattalin arzikin Najeriyar.