Kamfanin NNPC na Najeriya ya musanta cewa ya tallauce

Shugabankasar Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Tuni shugaba Goodluck Jonathan ya bada umarnin gudanar da bincike kan yadda ake sarrafa kudin kamfanin na NNPC

Babban kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya musanta cewa ya tsiyace.

Kamfanin yana maida martani ne ga wasu rahotanni da suka ambato ministan kudin kasar, Mista Remi Babalola a farkon wannan makon, yana cewa bashi ya yi wa kamfanin NNPCn kanta.

Kamfanin NNPCn ya ce, in ma ta biyo daga-daga, a yanzu haka yana bin gwamnatin Tarayya makudan kudade, na irin tallafin da take yi a bangaren albarkatun man petur.

Kamfanin mai na Najeriya, wato NNPC yana fama da zunzurutun cin hanci da rashawa da kuma rashin tsarin gudanawar na gaskiya.