An saka dokar hana yawon dare a Wukari

Taswirar Najeriya
Image caption Gwamnatin jahar Taraba ta saka dokar hana yawan dare biyo bayan barkewar rikicin addini a garin Wukari

Hukumomin jihar Taraba dake arewacin Najeriya sun kafa dokar hana yawon dare a garin Wukari inda mutane hudu suka rasa rayukansu kuma wasu da dama suka jikkata a jiya, sakamakon wani rikicin addini da ya barke.

Rundunar 'yan sandan jihar tace duk da cewa yanzu kura ta fara lafawa a garin na Wukari, ya zama dole kowa ya kasance a gida daga karfe shidda na yamma zuwa karfe shiddan safe.

Rundunar 'yan sandan jahar ta kara da cewar ta baza jami'an tsaro a ciki da kuma wajen Wukari dama jahar Taraban gabakidaya domin gudun kada rikicin ya tsallaka zuwa wasu jahohi dake da makwabtaka

Mahukunta a jihar Taraban dai sun ce rikicin na Wukari ya barke ne saboda rushe wani masallaci da wasu suka yi, lamarin da ya haddasa ramuyar gayya.

Rundunar 'yan sanda ta jihar Taraba a Nijeriya, ta tabbatar da mutuwar mutane hudu da kuma jikkata wasu da dama a rikicin addinin da aka yi a garin Wukari.