Argentina ta halalta auren jinsi daya

Majalisar dattijan kasar ce ta kada kuri'ar amincewa da hakan
Image caption Majalisar dattijan kasar ce ta kada kuri'ar amincewa da hakan

Argentina ta kasance kasar farko a yankin Latin Amurka da ta halalta cewa namiji na iya auren namiji, mace ta auri mace, bayan wata kuri'a da majalisar dattijan kasar ta kada.

'Yan majalisa talatin da uku ne suka amince, yayinda ashirin da bakwai suka nuna adawa da shirin dokar, wanda zai kuma baiwa irin wadannan ma'aurata damar daukar 'ya'ya na riko.

Wani dan majalisar Dattawan Argentinan, Sanata Gerardo Morales ya ce wannan doka za ta kawo sauyi ta bangaren al'ada, yana mai cewa za ta taimaka wajen gyara rashin adalci da wariyar da ake nuna wa wasu 'yan Argentina.

Cocin Roman Katolika, da 'yan Evengelica sun yi ta yekuwar nuna adawa da shirin dokar, suna cewa za ta tarwatsa iyali.