EFCC ta yi kiran a gujewa masu tabo a zabe mai zuwa

A Najeriya, shugabar hukumar EFCC, mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati,ta bukaci kungiyoyin farar-hula da su taimaka wajen wayar da kan jama'a, wajen hana kuru'unsu ga 'yan takarar da suka san cewa masu cin hanci da rashawa ne a zabubuka masu zuwa.

Mrs Farida Waziri ta ce dole a yi hakan idan dai ana son daidaita al'ammura a Nijeria.

Sai dai wasu na ganin cewa ba kowane dan Najeriya ne zai iya rarrabe maciya hanci da rashawa a tsakanin al`uma ba, ba tare da taimakon EFCC ba, kasancewar ita ce ke da alkaluman ire-iren mutanen da ta gurfanar gaban kuliya.

Amma Hukumar ta ce ba za ta fitar da jerin sunayen irin wadanan mutanen ba, kamar yadda ta yi a zaben 2007, saboda ba huruminta ba ne.