Hukumar zaben Najeriya zata fara taro a Uyo

Shugaban hukumar zaben najeriya Farfesa Attahiru Jega
Image caption Shugabannin hukumar zaben najeriya zasu fara wani taro yau a Uyo dake jahar Akwa Ibo

A Najeriya idan an jima ne shugabannin hukumar zaben ta kasa wato INEC zasu fara wani taro a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.

Shugabannin hukumar zasu soma tattaunawa ne akan yadda hukumar zaben zata bullowa kalubalen tsara zabukka masu zuwa a kasar.

Taron dai tsakanin kusoshin hukumar ta INEC ne, da suka hada da shugabanta, Farfesa Attahiru Jega da sauran kwamishinonin hukumar.

Taron dai shine mafi muhummmanci da shugabannin hukumar zasu gudanar akan tsare tsaren zabukka masu zuwa a kasar.

A yayinda babban zaben Najeriya ke gabatowa, hankalin 'yan kasar ya karkata dangane da yadda hukumar zaben zata shirya sahihin zabe na gaskiya