Hukumar zaben Nijer ta rage kasafin kudin ta

Taswirar Niger
Image caption Taswirar Niger

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a Niger, watau CENI, ya ce a yanzu suna bukatar CFA biliyan ashirin da tara ne domin shirya zabubuka a kasar, ba wai biliyan talatin din da suka sanar tun farko ba.

Shugaban Hukumar zaben, Mai sharia Abdourahmane Ghousmane ya ce hakan ya biyo bayan matakin da Hukumar ta dauka ne na soke zaben gundumomi - ko Departement - daga cikin zabubuka guda bakwai da ta shirya gudanarwa a kasar.

A watan janairu mai zuwa ne dai ake shirin gudanar da zaben shugaban kasar ta Niger, sannan a rantsar da shi a watan Maris.