An kama masu kokarin satar mutane a Kano

Yan sandan Najeriya
Image caption Yan sandan Najeriya

A Nigeria, rundunar yan sandan jahar Kano, ta bayyana cewa yanzu haka ta kame wasu mutane tara da ake zargi da shirin satar mutane dan neman a fanshe su da kudi.

Rundunar tace ta samu nasarar damke mutanen ne, bayan an tsegunta mata aniyarsu.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rundunar yan sandan kasar ke kara matsa kaimin kubutar da wasu 'yan jaridar da aka yi garkuwa da su a jahar Abia.

Yanzu haka dai hukumomin yansanda na kasar na fuskantar matsi saboda matsalar satar mutanen musamman a yankin kudu maso gabacin kasar.