Uganda ta ce za ta dauki fansa kan al-Shabab

Daya daga cikin gawar wadanda su ka rasa rayukansu
Image caption Daya daga cikin gawar wadanda su ka rasa rayukansu

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni ya ce kasar za ta dauki fansa a kan kungiyar 'yan kishin Islama ta Somalia wato Al-Shabab wacce ta dauki alhakin harin bom din da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 74.

Shugaban ya ce zai tura karin dakaru sama da dubu ashirin zuwa Somalia, domin su murkushe kungiyar ta Al-Shabab.

Al-Shabab dai ta dau alhakin kadamar da harin bam a Ugadan a wajen gidan kallon kwallon kafa, inda kuma ta ce ta yi hakan ne saboda gwamnatin Uganda na taimakawa dakarun kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afrika da ke Somalia.

Mista Museveni ya ce sauran kasashe za su tura sojojin su Mogadishu.

"Ina da kwarin gwiwa cewa za a sa mu karin dakaru, ganin cewa Al-Shabab ta tayarda hankalin duniya za a samu karin matakai daga kasashen duniya a kan kungiyar". In ji Museveni.

Akwai dakarun kasashen duniya karkashin Tarayyar Afrika sama da dubu biyar a Somalia, amma suna gudanarda ayukan agaji ne kawai ga jamar kasar.

Shugaba Museveni ya ce ya na son ayyukan kasashen su canza ta hanayar yaki da ta'adanci.

"Sojojin mu suna Mogadishu domin tsaron filin jirgin sama da kuma fadar Shugaban kasa."

"Muna son mu kai wa kungiyar hari domin abin da su ka yiwa jama'ar kasar mu". A cewar shugaba Museveni.