Halin da matasa ke ciki a birane

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da Muhalli ya bayyana cewa a kasarin jama'ar dake zaune a yankunan marasa galihu a 'kasashe masu tasowa na fama da matsaloli na rashin ngantaccen kiwon lafiya da ilimi.

A wani rahoto da ya fitar na shekarar 2010 zuwa 2011 kan halin da matasa a birane ke ciki, ofishin ya kuma yi gargadin cewa samar da tsaro da ci gaban 'kasashen duniya sun ta'allaka ne ga ingantaccen rayuwar jama'a musamman matasa.

Shi dai wannan rahoto na shekarar 2010 zuwa 2011 da ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da muhalli ya fitar kan halin da matasa a birane ke ciki, yayi nazari ne akan yanayin rayuwar jama'a musamman matasa a wasu manyan birane biyar a 'kasashe masu tasowa da suka hada da Brazil da Indiya da Kenya da Jamaica da kuma Najeriya.

Rahoton ya bayyana cewa akasarin matasa dake wadannan kasashen na fama ne matsaloli da suka hada da rashin samun ingantaccen muhalli, kiwon lafiya da kuma rashin samun ilimi mai nagarta wadanda kan kawo musu cikaswajen tafiyar da rayuwar su cikin walwala.

Image caption Matasa na fama da matsalar muhalli

Farfesa Ebanji Oyeyilaro Oyeyinka direktan bincike ne da sa ido na ofishin Majalisar Dinkin Duniya dake kula da Muhalli, ya kuma yiwa BBC 'karin bayani kan abin da rahoton ya gano a binciken da yayi dangane da yanayin rayuwar matasa a wasu biranen Najeriya.

"Alal misali a Najeriya mun gano cewa har yanzu akwai sauran aiki a gaba,idan aka duba ta fuskar muhalli mun ga cewa kusan kashi hamsin zasu sittin na 'yan Najeriya basu da ingantaccen muhalli ko kuma ace muhalli nasu na 'kashin kansu, kuma idan aka duba mataki mataki za'a ga cewa kusan kashi casa'in na matsalar da matasa ke fuskanta sun ta'allaka ne ga matsalar muhalli inda suke rayuwa da kuma rashin samun ingantaccen ilimi".

"koda yake an yi kokari ta wannan fuska, amma ta fuskar samun matasan da ke shiga makarantun gaba da piramare da kuma cike gibi dake tsakanin yawan matasa maza da mata dake shiga wadannan makarantun, har yanzu akwai saura aiki a gaba".

Dagane da batun ilimi da masu iya magana kan ce shine gishirin zaman duniya, rahoton ya lura da cewa koda yake akwai wasu fannonin da ake samu ci gaba, sai dai har yanzu akwai sauran aiki a gaba hukumomin Najeriyar wajen cimma burin muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa samar da ingantaccen tsaro da ci gaba a wadannan kasashe da suka hada da Najeriya sun ta'allaka ne ga samar da ingantaccen rayuwa ga jama'a musamman matasa a kasar.