Firaministar Australia ta kira sabon zabe

Makonni ukku bayan da ta dare mukamin Firaministar Australia, Misiz Julia Gillard ta yi kiran yin sabon zabe kafin karewar wa'adin gwamnatin na yanzu.

Ta ce yau da safe ta bukaci Babbar Gwamna ta kasar da ta rushe majalisar wakilai, domin a yi zaben majalisar, da kuma na rabin kujerun majalisar dattawa.

Za a gudanar da zaben ranar 21 ga watan gobe na Agusta.

A watan jiya ne Julia Gillard ta zama mace ta farko Firaministar Australia, bayan da ta kayar da wanda ta gada, Kevin Rudd, daga jagorancin jam'iyyusu ta Labour.

'Yan jam'iyyar dai sun razana ne cewa raguwar farin jininsa a kasar zai iya sanyawa su fadi a zabe na gaba.

A karkashin tsarin Firaminista na kasar, jagoran jam'iyya mafi rinjaye ne ke zama Firaminista.

Da take bayyana ranar zaben, Misiz Gillard ta ce jam'iyyar tata ce ta fi dacewa da sama wa Australiar makoma ta gari.