An kama mutane 5,000 bisa zargin caca

Katukan yin caca
Image caption Mutane da dama sun yi kaurin suna wajen caca a nahiyar Asiya

'Yan sanda sun kama fiye da mutane dubu biyar a nahiyar Asiya lokacin gasar cin kofin duniya da aka kammala a Afrika ta Kudu, bisa zargin yin caca ba bisa ka'ida ba.

Haka kuma an yi awangaba da kimanin dala miliyan goma a kasashen China da Malaysia da Singapore da Thailand, a cewar kungiyar 'yan sanda ta kasa da kasa.

'Yan sanda a kasashen "sun gano sannan suka kai sumame a kimanin dandalin caca 800", kamar yadda suka bayyana.

Dandalin 'yan cacar sun mikawa 'yan sanda zunzurutun kudi har dala miliyan 155 na caca.

A lokacin sumamen da suka kai a watan Juni da Juli, 'yan sanda sun kama kadarori da suka hada da motoci da katin kudi na banki, da na'urar kwamfiyuta da wayoyin salula.