Hukunci kan dukiyar dan Suharto a Indonesia

Tommy Suharto
Image caption Tommy Suharto

Kotun kolin Indonesia ta yanke hukuncin cewa gwamnatin kasar tana iya rike sama da dala miliyan dari da talatin da ta kwace daga Tommy Suharto, dan tsohon shugaban kasar.

Matsalar dai ta taso ne daga tsiyacewar kampanin kera motoci na Mr Suharton.

Masu aiko da rahotanni na cewa , hukuncin, wanda ya soke na baya, na nuna yadda fada-ajin da iyalan Suharton suke da shi yake raguwa.

An taba samun Tommy Suharto da laifin aikata kisan kai, a wata shari'ar ta daban, amma kuma tuni aka sake shi, yake kuma ci gaba da wasu harkokin kasuwancinsa.