Interpol ta kama mutane dubu biyar

Interpol
Image caption Interpol

Hukumar 'yan sanda ta duniya, Interpol, ta ce an kama mutanen da yawansu zasu kai dubu biyar a wasu kasashen Asiya hudu, bisa zargin cacar da ta saba ka'ida ba, a lokacin wasannin gasar cin kofin duniya ta kwallon kafa.

Wani jami'in hukumar ya ce an kai sumame a kan gidajen caca kimanin dari takwas a kasar China, ciki har da yankin Hong Kong da Macau, da kasar Thailand, da Malaysia da kuma Singapore, a lokacin gasar ta wata guda.

Waklin BBC ya ce sun kwace miliyoyin daloli na kudi, da motoci, da katunan banki, da kwamputoci da wayoyin salula.

Hukumar ta Interpol ta ce aikin yayi nasara, kuma akwai alaka tsakanin irin wannan caca kan wasanin kwallon kafa, da bad da sawun kudaden haram da kuma karuwanci.