Wata tsutsa mai illa ga gonaki ta ba'yana a jihar Jigawa

worms
Bayanan hoto,

Tsutsa

Tsutsa mai lahani ga gonaki ta bayana a jihar Jigawa

A jihar Jigawa dake Arewacin Najeriya wata tsutsa ta ba'yana, a gonakin sassan wasu kananan hukumomin jihar biyu, dake makwabtaka da jihar yobe da kuma jamhuriyar Nijar, inda take cinye shuka.

Kananan hukumomin da wannan tsutsa ta bayyana , sune Kirikasamma da Birniwa kuma kawo yanzu tayi barnar gaske, inda take cinye ridi da wake a gonaki da dama.

Wakilin BBC a jihar ya ce tsutsar tayi wa manoma da dama ta'annati.

Manoman sun ce a kwanakin baya ne, tsutsar ta kunno kai kuma a bara ma haka ta yi masu.

To sai dai Gwamnatin jihar ta ce tuni ta dauki matakin kawo karshensu.