An kasa cimma daidaito kan tsarin karba-karba

Shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Dr Nwodo
Image caption Batun tsarin karba-karba dai ya janyo muhawara mai zafi tsakanin 'yan jam'iyyar PDP

Wani taro da aka gudanar a Kaduna domin duba al'amurran da suka shafi siyasar yankin, musamman ma batun wanda zai tsaya takara karkashin jamiyyar PDP ya bar baya da kura.

Yayin da wasu, musamman wadanda suka shirya taron ke ganin lokaci yayi da za'a shure batun karba-karba a neman wanda zai kasance dan takarar jamiyyar PDP a zaben kasar na shekarar 2011, Wasu kuma musamman dattawan yankin, na ganin wannan labarin kanzon kurege ne kawai, domin a bisa tsarin na karba karba kudancin kasar ya yi mulki har na tsahon shekaru 8, a saboda haka ba su ga dalilin da zai sanya yanzu a sauya tsarin ba.

Taron dai wanda aka gudanar a jiya domin warware wannan batu, har yanzu za a iya cewa bai cimma nasarar warware wannan takaddama ba.