Sakin da aka yi ma Al Megrahi kuskure ne - inji Amurka da Birtaniya

Megarahi
Image caption Mista Megrahi da shugaban kasar Libya Mouammar Gaddafi

Hilary Clinton ta tattauna da takwaranta na Burtaniya su tattauna a wayar tarho

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton ta tattauna da takwaranta na Burtaniya William Hague dangane da sakin dan kasar Libyan nan Abdelbasit al-Megrahi, da aka samu da laifin dasa bom a jirgin Amurkan da ya fashe a garin Lockerbie na Scotland.

Sakatariyar harkokin wajen amurka ta ce mai yuwa Birtaniya zata so ta yi bayani ga majalisar dattawan kasar, akan abin da ya sa aka saki Almegrahi da wuri ba tare da ya kamala wa'adin da aka debar masa ,a gidan yari bisa aikata laifin sanya bam a jirgin saman amurka da ya fashe a lockerbie.

Madam Clinton na fuskantar fushin wasu sanatocci wadanda, a makon da muke ciki suka bukaci, ta kaddamar da bincike akan ko kamfanin mai na BP ya roki gwamnatin Birtaniya ta sako Mista Megrahi, domin kamfanin ya sami kwangilar hako mai a kasar Libya

Kamfanin na BP ya amince da cewa ya roki gwamnatin Birtaniya a shekerar 2007, wajen ganin Birtaniyar da Libya sun cimma matsaya akan batun sauya wa Megarahi wurin zama, sai dai ya nesanta kansa daga duk wata tattaunawa da ta shafi sakin mista Megrahi

A watan Augustan bara ne ministan shariar Scottland, ya saki Mista Megarahi saboda cuttar sankarar da yake fama da ita kuma a wancan lokacin an bayana cewa watanni uku ne kawai suka rage masa a duniya .