Musulmin Nijar sun koka kan dokar data hana amfani da nikab

masalaci
Image caption Masalaci a Jamhuriyar Nijar

Musulmin Nijar sun koka kan matakin da Faransa ta dauka

A jamhuriyar Nijar, wasu musulmin kasar sun nuna rashin jin dadinsu, dangane da dokar da kasar Faransa, ta dauka a baya bayan nan na hana mata musulmi da ke zaune a can sanya nikab.

Sun ce Faransa ta yi ma musulmi rashin adaci da dokar .

Musulmin Nijar sun kuma ce matakin ya keta dokokin kare hakkin dan adam, da kasashen duniya suka rattaba hannu a kansu.

Sun ce hukomomin Faransa nada wata munufa a kasa, shi yasa suka kawo wannan doka

Musulmin jamhuriyar Nijar sun kuma yi kira, ga mata musulmi dake Faransa akan kada su karaya da sabuwar dokar.