IFAD ta ce matsalar karancin abinci a Nijer ta munana

Ifad
Image caption Ifad

Babban Darektan dake kula da yankin Yammaci da Tsakiyar Afrika na Asusun habaka ayyukan noma a kasashen duniya, IFAD ko FIDA, ya ce matsalar karancin abincin da ake fama da ita a Jumhuriyar Nijer ta munana.

Ya bayyana haka ne a wani taro na manema labarai wanda aka gudanar ta hanyar na'ura mai kwalwala a birnin Rome.

Dr Mohammed Beavogui, ya ce mutane kusan miliyan bakwai ne a Nijer, watau rabin al'ummar kasar, ke fama da karancin abinci.

Ya ce bayanan da suke da su a hannu, sun nuna cewa matsalar ta yi munin gaske.

A cewar Dr Beavogui yankin Maradi shi yafi kowanne fama da wannan matsala saboda yawan jama'a da karancin filin noma.

A kwanan baya dai, Dr Beavoguin ya kai wata ziyara a Jumhuriyar ta Nijer don gane ma idanunsa halin da ake ciki a kasar ta Nijer.