Obama ya yi marhabin da nasarar da BP ya yi

Shugaba Obama
Image caption Mr Obama dai ya ce yana da muhimmanci kada a yi garaje

Shugaba Barack Obama yayi marhabin da nasarar da kampanin mai na BP ya samu ta dakatar da kwararar da mai ke yi daga wata rijiyar mai da ta barke a tekun Mexico.

Sai dai shugaba Obama ya ce har yanzu akwai sauran aiki a gaba.

Ya ce yana da muhimmanci kada a yi garaje, kuma daya daga cikin matsalolin sa na'urar daukar hoto a karkashin tekun, shi ne da zarar an ga mai ya daina yoyo sai ace, an kammala aiki , alhali kuwa aikin bai kare ba.

Tun da farko darajar hannayen jarin kampanin man na BP ya tashi sosai, bayan nasarar da ya samu wajen hana tsiyayar man a karon farko cikin watanni uku.