Kamfanin BP ya rufe rijiyar man da ke kwarara

Rijiyar man da ke tsiyaya
Image caption Wannan ne karo na farko da BP ya samu nasara tun watan Aprilu

Kamfanin man fetur na BP ya ce yayi nasarar rufe rijiyar da ke kwararar da mai, a mashigin tekun Mexico, a karo na farko bayan hadarin da ya haifar da malalar, watanni uku da suka shude.

A karon farko kusan watanni ukku da suka shude, nau'rorin daukar hoto da aka sa karkashin tekun sun nuna, babu man dake tsiyaya daga rijiyar mai data lalace.

Kamfanin ya ce an toshe wurin da man ke tsiyaya, kuma yana kan gudunar da wasu gwaje gwaje, domin tabatar da rufin da yayi ba zai janyo wata matsala ba.

Bayan an shafe sao'i 48 da gwaji, sanan kamfanin na BP zai yanke shawara kan matakin gaba da zai dauka.

Wanan ne mataki mafi girma da kamfanin ya cimma a yunkurin sa na ganin , ya dakatar da adadin mai dake tsiyaya a cikin teku wanda aka kiyasta cewa ya kai ganguna dubu talatin da biyar zuwa dubu sistin a kowace rana .