Jakadan Amurka a Sudan ya kai ziyara zuwa Uganda

Image caption Garin Juba a kudancin Sudan

Jakadan Amurka na musaman Sudan ya fara ziyarar makonnin biyu

A yau ake sa ran jakadan Amurka na musaman zuwa Sudan Scott Gartion, zai isa Khartoum babban birnin kasar a farkon ziyarar makonni biyu da zata kai shi ga kasashen Uganda da kuma Qatar.

Mista Gration zai gana da jami'an diplomasiya na majilisar Dinkin Duniya da gamayyar Afrika da kuma kasashen turai da dama.

Haka kuma zai gana da wakilan manyan jam'iyyun Sudan, da suka hada da National Congress Party ta shugaba Omar Al bashir da kuma tsofaffin, yan tawayen kudancin kasar SPLM.

Zai kuma ziyarci yankin Darfur da kuma garin juba baban birnin Kudancin Sudan.