WHO ta soki kungiyar Amnesty International

Taron Hukumar kiwon lafiya ta duniya
Image caption Taron Hukumar kiwon lafiya ta duniya

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta yi kakkausar suka kan wani rahoto da kungiyar kare hakin bil'adama ta Amnesty International ta fitar, wanda ke sukar lamirin tsarin kiwon lafiya na Korea ta Arewa.

Darakta Janar ta hukumar ta WHO, Margaret Chan, ta ce an gina galibin rahoton ne kan irin bahasin da aka samu daga wasu da suka fice daga kasar, wasunsu ma shekaru masu da dama da suka wuce.

Ta ce ba su yi la'akari da matakan inganta harkokin kiwon lafiyar da ake dauka a baya bayan nan ba.

Dr Chan wadda ta ziyarci Korea ta Arewa a cikin watan Aprilu, bisa gayyatar hukumomin kasar, ta kuma bayyana tsarin kiwon lafiyar a matsayin son kowa, kuma abin koyi ga kasashe masu tasowa, inda babu karancin likitoci, da nas nas.