Mutane kamar 7 ne aka kashe a jihar Filato

Taswirar Najeriya
Image caption An yi zargin halaka mutane da kona gidaje

A Najeriya, rundunar tsaro ta hadin gwiwa a Jihar Plateau, ta bayyana cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu a harin da wasu wadanda ba a san ko su wanene ba suka kai kauyen Maza da ke karamar hukumar Jos ta Gabas.

Rundunar ta kuma ce da isar dakarunta kauyen wadanda suka kai harin suka shige daji inda suka bace, al'amarin da ya sa ba a samu nasarar kama kowa ba.

Baya ga asarar rayuka, an kuma kona gidaje a harin da aka kai daren jiya.

An kona gidaje akalla guda tara.

Jihar ta Plateau ta yi ta fama da tashe-tashen hankula a 'yan watannin nan, al'amarin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.