A yau Mandela ke bikin cika shekaru 92

Mandela
Image caption Nelson Mandela a lokacin da ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin duniya

A yau Lahadi ne Nelson Mandela ke cika shekaru casa'in da biyu da haihuwa, kuma a karo na farko za'a yi bukuwan tunawa da ranar a fadin duniya.

A bara ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta amince da tunawa da ranar, a matsayin ranar Nelson Mandela ta duniya, domin tunawa da gudunmawar da tsohon shugaban na kasar Afrika ta kudu, ya bayar ta fannin zaman lafiya da yancin dan adam.

Ana kuma sa ran cewa mista Mandela zai gudunar da bikin da iyalinsa a gidan sa dake birnin Johannesburg .

Wakilin BBC ya ce ana bukatar mutane ne, da su yi ayyukan taimakon al'umma na tsawon mintuna sittin da bakwai don tunawa da shekaru sittin da bakwai da Mr Mandela ya kwashe, ya na gwagwarmayar tabbatar da dimokradiyya.