Wata kungiya a Najeriya tayi kira a sako Manjo Al moustapha

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Wata kungiya a Najeriya tayi kira ga shugaban kasar ya sako Manjo Al-mustapha

Kungiyar Association for Al mustapha to be free a Najeriya, ta yi kira ga shugaban kasar, Dakta Goodluck Jonathan da ya taimaka ya sako Manjo Hamza Al moustapha

Ta ce zata gudunar da gangami a karamar hukumar Sardauna dake jihar Adamawa, sanan daga bisani ta je Abuja inda zata gabatar da kokenta ga hukomomin da abin ya shafa.

Kakakin kungiyar Comrade Bala Yakubu ya fada ma BBC cewa, shekaru goma sha biyu kenan da manjo Al mustapha ke tsare kuma kawo yanzu ba'a same shi da aikata wani laifi ba.

Shi dai Manjo Almustahpa shine babban jami'in tsaro, a lokacin mulkin mariyagayi janarar Sani Abacha.