Kawancen CFDR ya cimma yarjejeniya a Nijar

Niger
Image caption Ko hadin kan zai tabbata?

A jamhuriyar Nijar, jam'iyun siyasa na tsohuwar gamayyar CFDR, wadanda suka yi adawa da shirin tazarce na tsohon shugaban kasar, Mamadu Tanja, sun kulla wani sabon kawance a tsakaninsu.

Sun yi hakan ne domin tunkarar zabubuka masu zuwa.

A karkashin wannan kawancen da suka kulla yau din nan a birnin Yamai, jam'iyun su 17 sun dauki alkawarin ci gaba da kasancewa tare, ta yadda za su mara ma daya daga cikin ‘yan takaransu baya a zagaye na 2 na zaben shugaban kasa mai zuwa.

Da haka ne suke fatar dan takarar da suke goyon baya zai yi nasara a kan na watakila jam’iyyar MNSD mai mulki a da, wadda sojin da ke mulki a kasar a halin yanzu suka hambarar.