ECOWAS ta kai agaji Nijar

Kungiyar ecowas
Image caption Akwai karin agaji tafe in ji Ecowas

A jamhuriyar Nijar, Kawancen Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika, ko kuma ECOWAS ko CEDEAO a takaice, ya kai ma kasar wani agajin kayayyakin abinci na darajar tsabar kudi Dala dubu dari biyu.

Shugaban Hukumar Zartarwa na kungiyar ta ECOWAS din, Mista James Victor Gbeho ya jagoranci tawagar.

Akalla kamar mutane milyan bakwai ne dai a kasar ta Nijar ke fama da matsalar yunwa.

An ce yunwa a kasar ta fi kamari a jihar Maradi, jihar da ita ce ta fi yawan jama’a a kasar.