Mutane sun rasu a jihar Diffa sanadini amai da gudawa

taswirar Nijar
Image caption Hukumomi sun ce suna daukar mataki

A jahar Diffa da ke jamhuriyar Nijar hukumomin kiwon lafiyar jahar sun bada sanarwar barkewar anobar amai da gudawa a wasu garuruwa biyu, Gadura da Doro.

A kalla mutane takwas ne suka riga mu gidan gaskiya sanadiyar wannan cuta , daga cikin mutane 149 da suka kamu da ita.

Ana jin dai sanadin hakan amfani ne da ruwa marar kyau da mutanen yankin ke yi, musamman a wannan lokaci na damina.

Hukumomi dai sun ce sun dauki dukkan matakan da suka dace don hana yaduwar cutar.

Wasu manazarta suna ganin dalilin bai rasa nasaba da yunwar da ake fama da ita a kasar – abinda ke sanya mutane cin hakukuwa iri-iri da ka iya jawo masu aman da gudawa.