Shugabanci nagari muke so- inji matasan Najeriya

Nigeria
Image caption Wasu yan Najeriya

Shugabanci na gari muke so- Inji matasan Najeriya

A Nigeria batun shugabanci na gari yanzu haka shine abinda kungiyoyin matasa, da masu rajin kare hakkin demokaradiyya ke ta fafitikar ganin ya tabbata, a yayin da ake tunkarar zaben shekara ta 2011.

Wannan kuwa ya biyo bayan abubuwan da zabubbukan da suka gabata suka haifar ne, inda galibi shuwagabannin da aka zaba ba kasafai suke cika alkawuran da suka yi lokacin yakin neman zabe ba.

Siyasar kudi itace tafi yin kaka gida,wajen dulmuyar da talakawa domin sayar da kuri'unsu, ba tare da sun yi la'akari da wanda ya kamata ya shugabance su ba.

Akan haka ne wata kungiyar matasa a Maiduguri wato Future Generation Group, ta fara matsa kaimin ganin sun ja hankulan yan uwansu matasan, game da rawar da ya kamata su taka a zaben badi.