Jami'ar Tarayyar Turai ta je Zirin Gaza

Catherine Ashton
Image caption An jiran Isra'ila ta amsa kiran karin sassauci

Shugabar tsara manufofin hulda da kasashen waje ta Tarayay Turai, Catherine Ashton, ta ce ya zama wajibi ga Isra'ila ta dauki matakan da suka zarta na sassaucin takunkumi a kan Zirin Gaza, ta bude kan iyakokin yankin baki daya.

Baroness Ashton , wadda ke ziyara a yankin, ta ce ya kamata a ce Palasdinawa da 'yancin walwala, suna kuma samun kayayakin masarufi na shiga suna kuma barin Zirin na Gaza.

Sami Abu Zuhri, shi ne kakakin kungiyar Palasdinawa ta Hamas.

Ya ce mun yi marhabin da wannan ziyara, ta ministar harkokin wajen tarayyar turai, kuma muna fatan ziyarar za ta kara jagorantar matsin lambar kasshen duniya kan dakarun mamaye domin su bude datsewar da suka yi mana.

Ba a dai shirya wata ganawa tsakanin Baroness Ashton da Hamas ba.