Mutane kimanin hamsin ne suka mutu a Iraki

Gawawwaki a cikin mota
Image caption Ana ta fama da irin wadannan hare-hare a kwanan nan

Mutane kimanin hamsin ne suka mutu a Iraki, sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake biyu da aka kai kan dakarun wata kungiyar sa kai ta 'yan Sunni mai suna Sahwa, wadda ke mara ma gwamnati baya.

Akalla mutane arba'in da uku ne aka kashe a birnin Bagadaza, lokacin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam din da ke jikinsa, yayin da jama'a ke cikin layi suna shirin karbar albashi a wani sansanin soji.

Shi kuma hari na biyu an kai shi ne a wani gari, kusa da kan iyakar Irakin da Syria, inda aka kashe mutane uku.

Shekaru hudu da suka wuce ne kungiyar ta Sahwa ta juya baya ga kungiyar Alka'ida, domin mara baya ga dakarun Amurka.