'Yan jaridar da aka saki sun koma gidajensu

Yansandan Najeriya
Image caption Saura kuma a kamo masu satar mutanen

Da yammacin yau ne 'yan jaridar da aka saki suka koma garuruwansu. Wadanda suka yi fashin su suke kuma neman kudin fansa sun sake su ne daren jiya bayan da suka ga babu sarki sai Allah.

Ttun ranar Lahadin da ta gabata ne aka yi garkuwa da mutanen a kusa da garin Aba na jihar Abiya.

Bayanai sun ce ba a biya fansa ba dai kafin a sako su.

Wani mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce babu wani kudin fansa da aka biya, duk kuwa da cewa tun farko wadanda suka sace mutanen sun bukaci a biya su sama da Dala miliyan guda kafin su sako su.

Uku daga cikin wadanda aka sacen jami'ai ne na kungiyar 'yan jarida ta kasa a Nijeriya; dayan kuma wani ma'aikacin gidan radiyo ne.

A bana, wannan shi ne karo na biyu da aka sace 'yan jarida aka kuma nemi kudadaen fansa a yankin.