Kawancen AFDR a Nijar ya gabatar da tsarin mulki

Taswirar Nijar
Image caption Ko gwamnati za ta kula da wannan gudummuwa

A jamhuriyar Niger dazu ne tsohuwar gammayyar jam'iyyu masu mulki a Niger da MNSD-NASSARA ke jagoranta, wato AFDR a takaice, ta bayyana ma manema labarai a birnin Yamai cewa, ta bayyana wani sabon kundin tsarin mulki ga majalisar mulkin sojan kasar ta NIjar.

Kundin tsarin mulkin ya kunshi baiwa shugaban kasar da aka zaba cikkaken iko, akasin wanda kwamitin da gwamnati ta nada ya shirya don gabatarwa ga jama'a su yi kuri'a a kai, wanda kuma ya tanadi raba iko tsakanin Shugaban kasa da Fira minista.

Wannan yunkuri dai wani bangare na gamayyar jam’iyyun da suka mulki kasar don ganin sun ba da tasu gudummuwa a muhawarar tsarin mulkin da ake ta yi a kasar a halin yanzu.