Afghanistan da Pakistan sun kulla yarjejeniya

Afghanistan,da Pakistan sun kulla yarjejeniyar kasuwanci
Image caption Kasashen biyu sun jaddada muhimmancin yarjeniyar

Kasashen Afghanistan da Pakistan sun sanya hannu a wata muhimmiyar yarjejeniyar kasuwanci a tsakanin su.

Yarjejeniyar da aka sanyawa hannun za ta baiwa manyan motocin daukar kayayyakin na Afghanistan damar ratsawa ta kasar Pakistan don kai kayayyaki zuwa kasar Indiya.

Kana kuma Afghanistan za ta samu damar amfani da tashoshin jiragen ruwan Pakistan don bunkasa kasuwanci tsakaninta da sauran kasashen duniya.

Ministan harkokin kudin Afghanistan,Omar Zakiwal ya ce yarjejeniyar alama ce da ke nuna cewa dangantaka tsakanin kasashen biyu na inganta cikin gaggawa. Wannan yarjejeniya na zuwa a lokacin da Sakatariyar harkokin kasashen wajen Amurka,Hillary Clinton ke ziyara a yankin.