An bukaci karin kudi ga yaki da ciwon Aids

Bill Clinton
Image caption Bill Clinton a taron AIDS a Vienna

Mutane biyun da suka yi fice a batun yaki da cutar HIV/AIDS ko SIDA a duniya sun yi kira da a kara kashe kudi ta hanyar da ya kamata wajen samar da magunguna da rigakafin cutar.

Tsohon shugaban Amurka, Bill Clinton yace a kasashe da dama ana dibar kudade da dama a biya wa mutane da yawa kudin shiga jiragen sama don zuwa taruka, ana biyan kudade masu yawa a kan ayyukan kwarraru.

Haka kuma ya ce, ana kashe kudade masu yawa wajen nazarce-nazarcen da ba a amfani da rahotanninsu.

Shima Mr. Bill Gates ya shaidawa BBC cewa akwai magunguna masu rahusa da ake samu, amma kuma za'a iya rage kudaden da ake kashewa wajen gudanarwa da kuma kula ta bin hanyoyi nagari.