Zumuncin Amurka da Pakistan ya karu.

Ministan harkokin wajen Pakistan, Shah Mahmood Qureshi, ya ce ra'ayi da bukatun Amurka da Pakistan sun kara zamowa daya a wannan lokaci fiye da koyaushe a baya.

Yana jawabi ne a wata ziyarar da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hilary Clinton, ta kai kasar.

Amurka ta bayyana wani sabon agaji ga Pakistan, wanda ya kai na kimanin daruruwan milyoyin daloli.

Masu nazari suka ce Amurka ta nema ta rage kaushin kin jinin Amurka a tsakanin al'ummar Pakistan, da kuma tabbatar da samun goyon baya a yakin da take yi da Alqa'ida da Taleban.