Mutane 40 sun halaka a India

Hadarin ya abku ne bayan da wani jirgi da ke tafe ya afkawa wanda ke tsaye a tasha
Image caption Jirgin kasan da ya yi hadari a India

A kalla mutane arba'in ne suka mutu a wani hadarin jirgin kasa da ya abku a jihar Bengal ta kasar Indiya.

Hadarin dai ya afku ne da jijjifin asubahi a lokacin da wani jirgi maisuna Uttar Banga express, dake kan hanyara ta zuwa Calcuta, ya bangaji wani jirgin da ke tsaye a tashar jiragen kasan lardin Birhum.

Karon ya yi muni sosai inda ya sa taragwan jiragen su ka manne.

Masu kai agajin gaggawa sun isa wajen da aka yi hadarin,inda suke kokarin fitar da fasinjojin da suka makale a cikin jiragen.

'Hukumomi na sa ido kan aikin agaji'

Masu kai agajin gaggawa sun isa wajen da aka yi hadarin,inda suke kokarin fitar da fasinjojin da suka makale a cikin jiragen.

Hukumomin tashar jiragen kasar na sa ido kan yadda agajin ke tafiya.

Shugaban rundunar 'yansandan yankin Humayun Kabir ya ce an gano gawawwakin mutane,sannan kuma an kai wadanda suka ji rauni asibiti.

Rahotannin sun ce dukkan jiragn dai na cike ne makil da mutane,wadanda ke kan hanyarsu zuwa birnin bayan sun kammala hutun kashen mako.