Shugaba Jonathan ya gana da Shugabannin kabilar Igbo

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban Najeriya, Dr Goodluck Jonathan ya gana da gwamnoni da kuma shugabannin al`umomin shiyyar kudu-maso-gabashin kasar.

Sun tattauna ne a kan matsalar satar mutanen da `yan bindiga ke yi a yankin.

Shugaban kasar dai ya nuna wa dattawan rashin jin dadinsa dangane da yadda matsalar sace-sacen mutanen ke yawaita a yankin.

Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta bari `yan bindigar su ci gaba da jefa rayuwar jama`a cikin kunci ba.

Sai dai dattawan sun ba da shawarar cewa samar da aikin yi ga matasan yankin ita ce sahihiyar hanyar shawo kan matsalar.