Musulmi sun shigar da kara a Jos

A Najeriya, yau ne wata kotun tarayya da ke zama a Jos, babban birnin Jihar Plateau ta saurari karar da al'ummar Musulmin Jihar suka shigar suna neman hukumar 'yansanda ta kasa, da kuma gwamnatin jihar su biya su diyyar naira miliyan dubu daya .

Suna neman diyya ne saboda kashe daruruwan Musulmi da suke zargin 'yan sandan da aikatawa, ko kuma taimaka wajen aikatawa a tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan rikicin sha bakwai ga watan Janairu.

Su ma Kiristocin Jihar sun shigar da makamanciyar wannan kara inda suke neman diyyar naira miliyan dubu daya, suna zargin cewa sakacin rundunar tsaro ne ya sa aka kashe Kiristoci aka kuma kona musu dukiyoyi a kauyen Dogo Na Hauwa.