Kano ce kan gaba wajen ta'ammali da miyagun kwayoyi

kayan maye
Image caption Irin kayayyakin mayen da jama'a ke amfani da su a Kano

Wani rahoto da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta futar ya nuna cewa jahar Kano, dake Arewa maso yammacin kasar ce kan gaba a wajen shan miyagun kwayoyi a kasar.

Rahoton ya bayyana cewa Jahar wacce ke da sama da mutane miliyan goma ta zama kan gaba wajen fataucin miyagun kwayoyi.

A wurare da dama ne a jahar ake cinikin kwayoyin a fili ba tare da boyewa ba, kuma matasa kama daga maza da mata da kuma kananan yara na shiga cikin harkokin sayarwa da kuma shan kayan sa maye daban daban.

Ko da dai hukumomi suna cewa suna iya bakin kokarinsu wajen kawar da wannan matsala da ta addabi jahar, amma mazauna unguwannin da ake hada hadar kayan sa mayen a wajensu suna ganin ya kamata hukumomin su kara kaimi.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, wanda ya bi diddigin lamarin yace jama'a a garin na kokawa kan yadda lamarin ke barazana musamman ga tarbiyyar yaransu.

Kididdiga

Rahoton na hukumar ta NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta fitar yayi la'akari ne da yawan mutanen da aka kama masu fataucin kwayoyi, da kuma yawan matasan da alkaluma ke nuna cewa sun tsunduma cikin wannan harka.

Image caption Jihar Kano na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya

A da dai anfi sanin maza da harkar shaye shaye amma yanzu lamarin ya hada harda mata, da ma 'yan makarantu musamman na gaba da Sakandire.

A yanzu zai yi wuya ka iya ware wata unguwa a cikin tsakiyar birnin Kano da za ka ce ba'a saida irin wadannnan kayan maye.

Harkar shaye shayen abubuwan da ke gusar da hankula musamman ga matasa da su ne kan gaba na daga abubuwan da ake hakkake za su iya zama cikas ga ci gaban ko wacce irin al'umma.

Dalilai da dama ne dai matasan ke bayarwa cewa su ke sa su fadawa harkar shaye shaye, wadanda suka hadar da kuncin rayuwa, da karamin karfi, da kuma wasu halaye da suka samu kansu a ciki.

Jama'a da dama dai na danganta shaye shayen da rashin tarbiyya, da kuma halin kuncin rayuwa.

Kayan maye

Ko da dai tabar wiwi itace masu shaye shayen suka fi amfani da ita, amma akwai sauran abubuwa da dama da matasan ke amfani da su dan kawar da hankulansu. Kamar Sholisho da Bula da Fetur da kashin Kadangare da magunguna irin su Tramol da Venelyn har ma da kwatami.

To ko me matasan dake tsunduma shaye shaye suke bayyanawa a matsayin dalilan da suka sa su zabar wannan hanya.

A cewar Dakta Abdullahi Mai Kano Madaki malami a sashin nazarin halayyar dan Adam a jami'ar Bayero da ke Kano:

Image caption Jama'a na shaye shaye a filin Allah Ta'ala a jihar ta Kano

Rashin tarbiyya da talauci su ne manyan dalilan da ke sa yaran cikin wannan mummunar halayya.

Masu lura da al'amura dai na ganin akwai gagarumin aiki a gaban hukumomi da kuma al'umma wajen tantance dalilan da suke sa matasan fadawa cikin al'amuran shaye shayen miyagun kwayoyi da nufin rage matsalar, musamman ma dai jahar Kano da ita ce a kace kan gaba a Najeriya wajen ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Tabar barewar al'amura

Yanda ake ta'ammali da miyagun kwayoyi a Kano ya kai matsayin da mutum zai iya zuwa duk wajen da ake sai da kwaya ko ganye ya saya a fili ba tare da yana jin kunyar jama'a suna ganinsa a matsayin mai shan miyagun kwayoyi ba.

Unguwanni irin su Ireland a kofar Nasarawa da Koki da kofar Dan Agundi da kofar na Isa da Tudun Murtala da kasuwar Takari a Burget da Fage layin Kamfala da Kofar Ruwa na daga dimbin wuraren da ake sayar da irin wadannan kayan maye a fili ba kunya ba tsoro.

Lamarin ya kai har an taba yin wata cacar shan kwayoyi masu dinbin yawa a cikin shayi a Kofar ruwa, inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar daya daga masu cacar.

Wani matashi da ke mu'amilla da kwayoyin ya shaidawa wakilin mu cewa, suna samun kwayoyin ne a kasuwar Sabon Gari.

kuma jin haka yasa wakilinmu garzayawa kasuwar ta Sabon Gari don jin ta bakin kwamitin rikon shugabancin kungiyar masu saida magani, ko suna sane da cewa ana saida haramtattun kaya a wajensu?

Inda Malam Yusuf Bala Kibiya mamba a kwamitin, ya musanta cewa suna saida miyagun kwayoyi.

Ya kara da cewa suna hukunta duk wanda aka samu yana saida kwayoyin da aka haramta kamar yadda tsarin kasuwar ya tanada.

Mafita

Barrister Patrick Kwetishe shine kwamandan hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Kano, kuma ya shaidawa BBC cewa duka tabar wiwin da ake amfani da ita a jihar, shigowa ake yi da ita.

Abin tambaya dai shi ne tunda har ba a shukawa da kuma sarrafa wadannan kayan maye a Kano, ta yaya? kuma ta ina ake shigo da su jahar? Kuma su waye ke shigo da su?

Samun amsar wadannan tambayoyi ba shakka zai taimaka wajen rage matsalar da yanzu haka ta fara zama jiki a jahar ta Kano, da akewa lakabi da Timbin Giwa ko me da kazo an fika.