An kaddamar da kundin kyuatta aikin jarida a Najar

Janar Salou Djibo
Image caption Janar Salou Djibo,Shugaban mulkin sojin Nijar

A jamhuriyar Nijar, hadadiyar kungiyar 'yan jarida ta kasar mai sa ido a kan aikin kafofin yada labarai don kyautata aikin jarida a kasar, ONIMED, tare da hadin giwar hukumomin kasar, sun kaddamar da wani sabon kundin da ya kunshi wasu sabbin dokokin tafiyar da aikin jarida.

Dokokin sun tanadi watsa labari masu tushe, da kauce ma cin hanci ko tozarta 'yan kasa.

Wallaffa wannan kundi dai ya biyo bayan rubuta wasu labarai marasa kan gado a kan wasu 'yan siyasa da wasu kafofofin yada labari suka soma yi, bayan janye dokar da ke kare 'yan jaridar Nijar din daga garkamewa kai tsaye da zaran an zarge su da aikata wani laifi.