Ana taro kan cutar AIDS a birnin Vienna

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce ya kamata mutanen da ke dauke da kwayar cutar HIV mai haddasa cutar AIDS ko SIDA, a soma yi masu magani da wuri, da zarar an fahimci suna da cutar.

Wata sanarwar da Hukumar Lafiyar ta fitar a wani taron aids da ake yi a birnin Vienna, ta ce kamar mutane milyan biyar da dubu dari biyu ne suka samu magunguna a kan cutar aids a bara, karin mutum milyan daya da dari biyu ke nan, idan an kwatanta da bara waccan, wato 2008.

Ana wannan taro ne a daidai lokacin da ake ci gaba da nuna fargaba game da yuwuwar zabtare kudaden da kasashe masu bada agaji ke bayarwa domin yaki da cutar.