Tsarin tattara bayanan sirrin Amurka ba shi da sahihanci,inji jaridar Washington Post

Tambarin Ofishin Daraktan tsaron ciki na kasa a Amurka
Image caption Tambarin Ofishin Daraktan tsaron ciki na kasa a Amurka

Binciken da wata jarida ta gudanar a Amurka ya bayyana cewa, tsarin tattara bayanan sirri da kasar ta kirkira, tun bayan harin sha daya ga watan satumbar shekara ta 2001, ya yi wani girman da ba za a iya tantance sahihancinsa ba.

Jaridar Washington Post ta ce hukumomin Gwamnati da masu zaman kansu fiye da dubu 3 ne suke da hannu a tsarin tsaron mai girma ta yadda babu wanda ya san kudin da ya ci da ko mutane nawa aka dauka aiki ko kuma hukumomi nawa suka yi aiki iri daya.

Gwamnatin Amurka dai ta ce rahoton zai iya taimakawa abokan gabarta gano cibiyoyin tattara bayanan sirri, to amm ba ta warware babbar tuhumar da jaridar ta yi na babban rashin nagarta ba.