Afghanistan na son lura da sha'anin tsaronta-In ji Karzai

Tambarin dake nuni da taro kan tsaron Afghanistan
Image caption Afghanistan na son lura da al'amuran tsaron kanta

Shugaban kasar Afghanistan, Hamid Karzai ya ce kasar na son daukar alhakin samar da tsaron kanta nan da shekarar 2014.

Shugaban ya yi wannan bayani a lokacin da yake jawabin bude taron kasashen duniya na farko, da aka fara yau a kasar ta Afghanistan.

Ya ce dukkaninsu na fuskanta abokin gaba daya ne, wanda ke neman raba hadin kan kasashen.

A nasa bangaren, babban sakataren Majalisar dinkin duniya Ban Ki-Moon ya ce a baya kasashen duniya daban- daban sun yi kokarin samar da zaman lafiya ba tare da sanya jama'ar kasar a tsare-tsarensu ba.

Afghanistan dai ta karbi tallafin dala biliyan 36 tun daga shekarar 2001,sai dai ba su yi wani tasirin a zo a gani a kasar ba.

An kashe akasarin tallafin wajen tabbatar da tsaron kasar.

Wakilai daga kimanin kasashe saba'in ne ke halartar taron.